Labarai
Kebbi: Ƴan sanda sun ceto mutane 7 daga hannun ƴan bindiga
Rundunar ƴan sandan Jihar Kebbi, ta bayyana cewa jami’anta sun ceto wasu mutuane bakwai waɗanda Ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a garuruwan Bena-Mairairai da Ruwan Kanwa a jihar.
Kwamashinan ƴan Sandan jihar Ahmed Magaji Kwantagora, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a Birnin Kebbi.
Ya ce, ƴan bindigar sun tare hanyar shiga gari Bena-Mairairai ne, Sai dai bayan samun rahoto ne Ƴan sanda suka yi musu dirar mikiya.
Haka kuma ya ƙara da cewa “Bayan fafatawa da ɓara garin mun yi nasarar ceto Jamila Ahamad, da Shamsiya Ahamad, da kuma Tasi’u Haruna.”
Ƙwamishinan Ƴan sandan na jihar Kebbi, ya ƙara da cewa, rundunar ta kuma samu nasarar ceto wasu mutane huɗu a yankin ƙaramar hukumar Jega ta jihar waɗanda su ma ƴan bindiga suka yi garkuwa da su.
Haka kuma, ya ce, yayin samamen, ƴan sanda sun yi ƙwace wata mota ƙirar Toyota Corolla a hannun ɓata garin.
