Kasuwanci
CBN ya ƙara wa’adin daina amfani da tsofaffin kuɗi
Babban bankin Najeriya CBN, ya ƙara wa’adin daina amfani da tsofaffin takardun kuɗi.
Gwamnan CBN Mista Godwin Emiefele ne ya bayyana hakan a ganawarsa da manema labarai yau Lahadi.
A cewar Emiefele Ya ce ya samu amincewar yin ƙarin lokacin ne daga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Mista Godwin Emiefele ya ƙara da cewa za a daina karɓar tsofaffin kuɗin ne a ranar 10 ga watan gobe na Fabarairu maimakon ranar 31 ga wannan watan da muke ciki na Janairu.
