Nadin dai ya zo ne ƙasa da kwanaki bakwai da rasuwar Sarkin Dutse, Nuhu Muhammadu Sanusi.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa, Daga bisani an miƙa rahoton amincewar ga majalisar sarakunan jihar wadda ita ma ta amince da matakin da masu naɗa sarkin su ka ɗauka.
Haka kuma ta ruwaito cewa, Majalisar sarakunan ta aike da sunan Muhammad Hameem, wanda ɗa ne ga marigayi Sarkin Dutse da sauran ƴan takara biyu zuwa wajen neman amincewa.
A cikin sakon fatan alheri ga sabon sarki, Gwamna Badaru ya taya sarkin murna tare da yi masa fatan Allah ya yi masa jagora.
