Labarai
Ku Kawo Mana Rahoton Duk wanda Yaƙi Karbar Tsohon Kudi – Gwamnan Neja
Gwamnatin jihar Neja ta umarci ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a jihar da su kama mutanen da suka ki amincewa da karbar tsohon kudi a yayin cinikiyya.
Sakataren gwamnatin jihar Neja, Alh. Ahmed Ibrahim Matane ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a Minna a ranar Litinin. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Ya bayyana cewa har yanzu karbar tsoffin takardun naira na nan daram kuma duk wanda aka kama ya ki karban su domin yin kasuwanci to zai fuskanci fushin doka.
A cewarsa, “Tsoffin takardun naira na nan daram kuma duk wanda aka kama ya ki karba yana jawo wa ‘yan kasa wahala za a kama shi kuma a gurfanar da shi a gaban kuliya.”
Daga nan sai ya bukaci al’ummar jihar nan da su gudanar da harkokinsu na halal, sannan su kai rahoton duk mutumin da ya ki karban kudin ga jami’an tsaro a jihar domin daukar matakin da ya dace.
Rashin samun sabbin takardun takardun kudin da aka sauyawa fasali, ya janyo wa jama’a kunci, ganin yadda ‘yan kasuwa suka ki karban tsofaffin takardun naira, tare da dagewa a kan sabbi a matsayin hanyar musayar kudi.
