Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar, ya yi nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa a jihar Katsina.
Sakamakon da aka gabatar a zauren tattara sakamakon ƴan takarar shugaban ƙasa birnin tarayya Abuja, ya nuna alƙaluman da jam’iyyun APC da LP da NNPP da kuma PDP suka samu kamar haka.
APC 482,283
LP 6,376
NNPP 69,386
PDP 489,045
