Labarai
Kotun ƙoli ta tabbatar da Rufa’i Sani Hanga a matsayin Sanatan Kano ta tsakiya
Kotun Ƙolin Najeriya, ta tabbatar da Sanata Rufa’i Sani Hanga a matsayin dan takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar NNPP, kuma wanda ya lashe zaɓe.
Kotun ƙarƙashin Mai shari’a Uwani Abba Aji, ta tabbatar da hukuncin ne a yau Juma’a.
Haka kuma ta cikin hukuncin, Kotun ta umarci INEC da ta karɓi Sanata Hanga maimakon Sanata Malam Ibrahim Shekarau da ta bai wa nasara a baya.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, Kotun ƙolin ta kuma yi watsi da Shekarau a matsayin ɗan takarar jam’iyyar NNPP a takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya.
