Siyasa
An zaɓi Gwamna Inuwa Yahaya a matsayin shugaban ƙungiyar NGF
An zaɓi Gwamnan jihar Gombe Inuwa Yahaya, a matsayin sabon shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewa watau NGF.
Rahotonni sun bayyana cewa, an fara zaɓar Gwamna Inuwa Yahaya a matsayin gwamnan jihar ta Gombe ne tun a shekarar 2019.
Bayan zaɓen nasa, Gwamnan zai karɓi ragamar mulki daga hannun shugaban kungiyar mai barin gado Gwamnan jihar Filato Mista Simon Lalong.
Gwamna Inuwa Yahaya, ya lashe zaɓe a karo na biyu bayan da ya sake tsayawa takara a zaɓen bana.
