Siyasa
An zaɓi Godswill Akpabio a matsayin shugaban Majalisar Dattawa
Godswill Akpabio ya yi nasarar zama shugaban Majalisar Dattawan Najeriya bayan kaɗa ƙuri’a daga sabbin ƴan majalisar a yau Talata.
Akawun majalisar dattijai ne ya bayyana sakamakon zaɓen da ƴan majalisar suka kaɗa, inda ya ce Sanata Godswill Akpabio ne ya yi nasara da rinjayen ƙuri’a 63.
