Featured
Ƴan sanda sun kama mutanen da ake zargi da satar mutane a jihar Bauchi
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta cafke sama da mutane 100 da ake zargi da laifin satar mutane, fashi da makami da wasu laifuka.
Kwamishinan ‘yan sanda, Auwal Muhammad ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai ranar Litinin a Bauchi.
Ya ce rundunar ta kwato bindigogi; bindiga kirar gida, revolver, gatari, wukake, kwalabe, da dai sauransu daga wadanda ake zargin.
Ya ce rundunar na ci gaba da gudanar da ayyuka kan sahihan bayanan sirri da dabarun magance miyagun laifuka a jihar.
Ya kuma nanata kudurin Sufeto-Janar na ‘yan sanda (IGP), Kayode Egbetekun na karfafa alaka tsakanin ‘yan sanda da al’umma da inganta bayanan sirri don magance matsalolin tsaro a kasar nan.
