Featured
Gwamnatin Kano ta sake tura ɗalibai 50 ƙaro karatu zuwa ƙasar India.
A yau Juma’a Kashi na biyar na dalibai 50 daga cikin dalibai 1,100 da suka kammala karatun digiri na farko da gwamnatin jihar Kano ta ɗauki nauyin karatunsu a kasashen waje, sun tashi zuwa kasar Indiya domin yin karatun digiri na biyu a fannoni daban-daban.
Waɗanda suka ci gajiyar shirin sun tashi daga filin jirgin saman Malam Aminu Kano zuwa Legas a cikin jirgin Max Air da misalin karfe 7:30 na safiyar ranar Juma’a, inda kwamishinan ilimi mai zurfi Dakta Yusuf Ƙofar Mata da sauran jami’an gwamnati suka halarcin bikin tashin na su.
