Featured
Wasilah Ibrahim Ladan ta zama Sakatariyar ƙungiyar NAWOJ ta ƙasa
Hajiya Aisha Ibrahim Bura ta lashe zaɓen shugabancin Kungiyar mata ‘yan jaridu ta ƙasa wato NAWOJ wanda aka gudanar aka gudanar a birnin taraiyya Abuja a jiya Asabar.
Aisha Bura ta bayyana farin cikinta game da lashe zaɓen da tayi, inda ta ce za tayi duk mai yiwuwa wajen ganin tayi aikin da zai kawo ci gaba a ƙungiyar NAWOJ.
Itama a nata ɓangaren Hajiya Wasila Ladan tayi godiya ga Allah bisa lashe zaɓen da tayi a matsayin Sakatariyar Ƙungiyar NAWOJ ta ƙasa reshen jihar Kano.
Sannan ta ƙara da cewa gwamnatinsu za ta kwatanta adalci tare da sauke nauyin da Allah ya Dora musu.
