Connect with us

Featured

Kaduna: Sojojin Najeriya sun ƙwato makamai da mashina a hannun ƴan bindiga

Rundunar Sojin Najeriya ta 1, ta sanar da nasarar ƙwato tarin makamai da mashina daga hannun ‘yan bindigar daji a jihar Kaduna ta arewacin kasar yayin sumamen da suka kai wata maboyarsu a cikin daji.

Wata sanarwar Rundunar dauke da sa hannun mukaddashin jami’in hulda da jama’a na rundunar, Laftanar Kanal Musa Yahaya ce ke sanar da wannan nasara a sumamen wanda sojojin suka kai jiya Talata.

Musa ya ce bayan samun wasu bayanan sirri da kuma yunkurin da rundunar ke yi na ganin ta kakkabe ‘yan bindiga daga dazukan jihar kaduna, dakarun rundunar da hadin gwuiwa na ”Yan bangar jihar sun yi wa ‘yan bindigar kwanton bauna a yankin Dogon Dawa zuwa Damari, ko da ya ke ‘yan bindigar sun tsere cikin tsakar daji bayan luguden wutar da suka sha.

A cewar jami’in ” Bayan bincike dajin sai dakarun mu su ka gano bindigogin Fistil kirar Bareta da Ak 47 da kuma tarin alburusai.”

Haka zalika, dakarun rundunar da ke kula da kwanar mutuwa a karamar hukumar Birnin Gwari bayan samun bayanan sirrin cewa ‘yan bindiga sun shigo yankin, nan ta ke, Sojoji suka tunkaresu suka kuma tarwatsa su, ‘yan bindigan dai sun tsere bayan sun fahimci cewa an fi karfin su.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet