Featured
Rundunar Ƴan Sandan Jihar Kano Ta Kama Mutane 92 Kan Zargin Aikata Laifuka
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta cafke mutane 92 da ake zarginsu da aikata laifuka mabambanta a cikin makonni uku da suka gabata.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da waɗanda ake zargin ga manema labarai a jiya Litinin 02 ga watan Satumba, 2024.
Wadanda ake zargin sun hada da masu garkuwa da mutane, yan fashi da makami, barayin ababen hawa da kuma yan daba cikinsu harda marigayi Abba Burakita, da rundunar ta ke nema ruwa a jallo bisa zargin aikata fashi da makami.
SP Kiyawa, ya ce wannan nasarar ta samu ne bisa jajircewar jami’ansu da suka nuna kwarewa, don tabbatar da kare rayukan al’umma da kuma dukiyoyinsu.
Rundunar ta kama wadanda ake zargi da aikata fashi su 16, masu garkuwa da mutane 3, barayi 7, Dilolin kwaya 6, yan Damfara 7,Barayin motoci 6 da kuma yan Daba 47.
