Featured
Rundunar Ƴansandan Jihar Kano Za Ta Gudanar Da Atisayen Harbin Bindiga
Rundunar Yan Sandan jihar Kano sashin kwantar da tarzoma, za su gudanar da atisayen Harbin Bindiga, a ranar Alhamis 5 ga watan Satumba da juma’a 6 ga watan Satumban 2024.
Kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labari a ranar Talata.
Ya ce Yan Sandan kwantar da tarzoma mai lamba 52 dake Challawa, sune za su gudanar da atisayen Harbin Bindigar, a kebantaccen wurin nan hawan Kalebawa, dake karamar hukumar Dawakin Tofa.
SP Abdullahi Kiyawa ya kara da cewa za a fara atisayen harbin tun daga karfe 6:00 na safe zuwa 6:00 na yammacin wadannan ranakun.
KAKAKi24, ta ruwaito cewa kwamishinan yan Sandan jihar CP Salman Dogo Garba, ya shawarci mazauna yankin musamman Danbazau, Gangaren Dutse, Tumfafi, Kakurum da Dandalan dake kananan hukumomin Dawakin Tofa da kuma Ungoggo, da su kauracewa wajen kuma kar su firgita da karar harbin da za suji har sai an kammala.
