Featured
Sabbin Shugabannin NAWOJ Sunyi Alƙawarin Kawo Cigaba Ga Mata Ƴan Jarida
Ƙungiyar ƴan jaridu mata ta ƙasa reshen jihar kano NAWOJ, ta rantsar da sabbin shugabannin ta, a wani biki da ta shirya a Kano
Barista Adama daga ma’aikatar Shari’a ta jihar kano, itace ta jagoranci bikin rantsuwar, tare da mika jagorancin kungiyar ga sababbin Shugabannin da aka zaba.
Ƙwararriyar ƴar jarida daga ma’aikatar yaɗa labarai ta jihar kano, Bahijja Malam Kabara, ita aka rantsar a matsayin Sabuwar shugabar Kungiyar.
Da take jawabi yayin bikin rantsuwar, Kabara ta bayyana irin cigaban da zata kawo a bangaren sadarwa, musamman ga mata ƴan jarida.
Ta kuma bayyana muhimman abubuwan da kungiyar zata sa a gaba, wadanda suka hada da horar da mata ƴan jarida, da kuma kyautata alaka da gwamnati wajen inganta walwalar mata da ƙananan Yara.
Taron ya samu halartar manyan mutane ciki har da Aisha K Burra, Shugabar kungiyar mata ƴan jaridu ta kasa, da Wasila Ladan, Sakatariyar kungiyar ta kasa, sai Abdulrazaq Bello Kaura, Sakataren Shiyya na kungiyar Yan jaridu ta Najeriya.
Manyan baƙin sun nuna ƙwarin gwiwar su akan sababbin shugabannin, inda suka yi musu fatan ciyar da kungiyar gaba.
Sabbin Shugabannin da aka rantsar su ne :
Bahijja Malam Kabara – Shugaba (ma’aikatar yaɗa labarai ta jihar Kano)
Halima Yusuf Angulu – Mataimakiyar Shugaba (Pyramid Radio)
Maryam Muhammad Yakasai – Sakatariya (Kano State Radio)
Aisha Muhammad Yalleman – Mataimakiyar Sakatariya (Freedom Radio)
Hauwa Mustapha – Sakatariyar Kudi (Voice of Nigeria)
Rabi Bature – Ma’aji (ARTV)
Binta Kabir Usman – Mai binciken kuɗi (Kano Ministry of Information).
