Connect with us

Featured

Ƴan Kasuwa Na Da Damar Siyan Mai A Matatar Ɗangote – NNPC

Babban kamfanin mai na Najeriya, NNPCL ya musanta zargin da ya ce ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta Najeriya, MURIC ta yi masa na yi wa matatar mai ta Dangote maƙarƙashiya.

MURIC ta yi zargin cewa ƙarin kuɗin mai da NNPCL ya sanar a baya-bayan nan zai hana matatar Dangoten sayar da man a farashi mai rahusa, sannan ta yi zargin cewa kamfanin NNPCL ne kawai zai riƙa sayen mai daga matatar.

To sai dai cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Asabar 07 ga satumba, ya musanta zargin, yana mai cewa kasuwa ce ke ƙayyade farashin man kowace matata ciki kuwa har da ta Dangote.

”Ƙarin kuɗin mai da aka samu a baya-bayan nan ba zai hana matatar Dangote ko duk wata matata a cikin ƙasar nan samun ciniki ba. Idan ma suna ganin kamar kuɗin ya yi yawa, to matatar ta samu damar da za ta iya rage farashi domin samun ciniki a kasuwa”, in ji sanarwar.

Haka kuma NNPCL ɗin ya ce babu tabbacin samun ragin farashin kan man da aka tace a gida fiye da yadda ake sayar da shi a kasuwar duniya, kamar yadda matatar Dangoten ta tabbatar masa.

Kamfanin NNPCL, ya ƙara da cewa zai sayi man Dangote ne kawai idan farashin man a kasuwar duniya ya fi yadda ake sayar da shi a Najeriya, don haka matatar Dangote da sauran matatun cikin gida na da damar sayar da man ga duk wanda ke buƙata a kan farashin da suka daidaita.

”NNPCL ba shi da niyyar kankane sayar da man shi kaɗai a fagen kasuwancin da kowa ke da damar shiga a dama da shi, don haka maganar a ce NNPCL ne zai sayi mai daga matatar ba ta taso ba,” in ji sanarwa.

Kamfanin ya kuma ce babu ta yadda zai yi maƙarƙashiya ga kasuwancin da ya zuba hannun jarin biliyoyin daloli a cikinsa

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet