Connect with us

Featured

Ƙasar Nijar Ta Janye Daga Rundunar (MNJTF) Mai Yaki Da Boko Haram

 

Rundunar sojin Nijar ta sanar da janyewarta daga rundunar da ke yaki da masu da’awar jihadi a yankin tafkin Chadi, rundunar MNJTF a ranar Asabar da yamma.

A cikin 2015, Najeriya, Chadi, Kamaru da Nijar sun sake farfado da rundunar hadin gwiwa ta Multinational Joint Task Force (MNJTF), wacce aka kirkira a shekarar 1994 don yaki da kungiyoyin jihadi a kewayen tafkin Chadi.

Tafkin Chadi ruwa da ya ratsa kasashe hudu, ya zama sansanin mayakan jihadi, inda ya ke ba da mafaka ga mayakan Boko Haram da na IS a yammacin Afirka (ISWAP).

Wannan janyewar “yana nuna sha’awar karfafa tsaro a wuraren mai a Arewa,” in ji sojojin Nijar, wanda ake la’akari da daya daga cikin manyan ginshikan MNJTF.

Kamfanonin man da ke yankin Diffa (kudu maso gabas) na fuskantar barazana daga kungiyoyi masu dauke da makamai masu adawa da hukumomin na Nijar wadanda ke kai hare-hare musamman kan babban bututun mai da ke dauke da danyen mai zuwa makwabciyar kasar Benin.

Dangantaka tsakanin jihohi ya raunana gwagwarmayar yaki da masu dauke da makamai a yankin a cikin kungiyar ta MNJTF.

Tun bayan juyin mulki a Nijar da aka yi a watan Yulin 2023, majalisar soji ta CNSP ta zargi Najeriya da bai wa sojojin kasashen waje mafaka domin tada zaune tsaye, lamarin da Najeriya ke musantawa.

Bayan shafe sama da shekara daya ana kai ruwa rana, makwabtan biyu sun sanar da dawo da hadin gwiwar soji a watan Agustan 2024, a ziyarar da babban hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Christopher Musa ya kai birnin Yamai.

“Matsalar ita ce wasu na yin kokari, wasu kuma suna yi musu zagon kasa, dole ne mu hada kai mu kawo karshen tsoma bakin kasashen waje a yankinmu,” in ji gwamnan yankin Diffa, Janar Mahamadou Ibrahim Bagadoma, a wani taron yankin da aka gudanar a Maiduguri, a arewa maso gabashin Najeriya, a farkon watan Fabrairu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet