Featured
Ku Kasance Cikin Shiri Don Yaƙar Ta’addanci, Saƙon Shugaban Sojin Kasa Ga Sabbin Sojoji
Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya bukaci sabbin sojoji da suka kammala horo a Zaria, Jihar Kaduna, da su kasance a koda yaushe cikin shiri don fuskantar kalubalen ta’addanci da tarzoma a ƙasar nan.
Yayin jawabi a bikin yaye sabbin sojoji 6,195 na rukuni na 88 a ranar Asabar 14 ga Yuni, 2025. Oluyede ya jaddada muhimmancin kiyaye ƙa’idodin da ɗabi’un rundunar Sojin Najeriya.
Ya ce rayuwar soja rayuwace ta sadaukarwa da kishin ƙasa, inda ya tunatar da su cewa Sojin Najeriya ƙungiya ce mai ƙwarewa wacce aka dora mata alhakin kare iyakokin ƙasa da tabbatar da zaman lafiya da tsaro.
Ya kuma bayyana musu cewa, “Yayin da kuke barin Depot yau don shiga wannan aikin gagarumi, ku sani cewa zaku kasance cikin sahun gaba wajen warware matsalolin ta’addanci da tarzoma da ƙasa ke fuskanta. Don haka, duk inda aka tura ku, dole ne ayyukanku su nuna horon da kuka samu, ku kuma nuna jarunta a lokacin wahala.”
A ƙarshe, Oluyede ya nuna godiyarsa ga Shugaban ƙasa kuma Kwamandan rundunar soji ta ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da sauran masu ruwa da tsaki saboda irin goyon bayan da suke ba wa Sojin Najeriya.
