Featured
Gwamnan Bauchi Ya Naɗa Ɗan Ƙasar China a Matsayin Mai Bashi Shawara Kan Tattalin Arziƙi
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya nada wani ɗan ƙasar Sin, Mista Li Zhensheng, a matsayin mai ba da shawara kan harkokin tattalin arziki ga gwamnatin jihar.
Mohammed ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis 14 ga Agusta yayin rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da cibiyar China Global Promotion Cooperation Research Centre a Bauchi.
A cewarsa, wannan mataki na nufin ɗaga matsayin Bauchi zuwa cibiyar haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa, tare da burin dogon lokaci na zuba jari, bunƙasa ayyukan gina muhalli da ababen more rayuwa, da kuma ƙarfafa haɗin kan bangarori daban-daban kamar noma, ilimi, kiwon lafiya, masana’antu, hakar ma’adinai, man fetur da iskar gas, da sauƙaƙe harkokin kasuwanci.
Yarjejeniyar ta ƙunshi tsari na haɗin gwiwa, inda za a ƙirƙiri takamaiman yarjejeniyoyi na kowane aiki daban-daban bisa ga yanayi.
“Wani ɓangare na wannan yarjejeniya shi ne kafa Ofishin Wakilai na Jihar Bauchi a ƙasar Sin domin sa ido kan aiwatar da ayyuka da tabbatar da kammalawarsu cikin lokaci,” in ji gwamnan.
Mohammed ya bayyana cewa haɗin gwiwar ya yi daidai da tsarin diflomasiyya tsakanin Shugaban ƙasar Sin, Xi Jinping, da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, wanda manufarsa ita ce ƙarfafa dangantaka tsakanin matakin ƙasa da kuma jihohi.
“Wannan yarjejeniya ba wai kan ayyukan gine-gine kaɗai take ba — kan sauya rayuwa take. Muna buɗe ƙofar Bauchi ga duniya,” in ji shi, yana mai cewa haɗin gwiwar zai ƙara yawan zuba jari daga waje, samar da ayyukan yi, haɓaka ƙwarewa, sabunta muhimman bangarori, da inganta matsayin Bauchi a idon duniya.
A nasa jawabin, Zhensheng, wanda shi ne Shugaban China Global Promotion Cooperation Research Centre, ya yi alkawarin cewa cibiyar za ta yi duk mai yiwuwa wajen samar da albarkatun duniya don tallafa wa sauyin tattalin arzikin Bauchi.
“Muna da niyyar taimaka wa Bauchi wajen cimma ci gaban dorewa, samun ingantattun ababen more rayuwa, da inganta rayuwar jama’a,” in ji shi.
