Connect with us

Featured

Ƴan Najeriya Za Su Fara Samun Wutar Lantarki Awa 24 A Kullum – Ministan Lantarki

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa Najeriya tana dab da samun ci gaba mai ɗorewa a harkar samar da wutar lantarki, tare da shirin tabbatar da wuta ba tare da yankewa ba a kowace rana. Ministan Wuta, Adebayo Adelabu, ya bayyana haka a Abuja yayin kaddamar da sabbin gine-gine guda biyu da ke ɗauke da ɗakunan koyarwa guda biyar da wajen kwana mai ɗakuna 104 a Cibiyar Horar da Ma’aikatan Wuta ta Ƙasa (NAPTIN). Ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta nuna gamsasshiyar niyya ta hanyar juya manufofi zuwa aiki.

Adelabu ya bayyana cewa ƙasar ta cimma mafi girman adadin samar da wuta da isar da ita a tarihi, wanda ya nuna akwai alamu na samun sauyi a fannin. Ya ce a cikin ɗan lokaci Najeriya za ta shiga jerin ƙasashe masu wuta 24/7 ba tare da katsewa ba. Ministan ya ƙara da cewa gwamnati na cigaba da samar da wuta ga jami’o’i, asibitoci, cibiyoyin kiwon lafiya da sauran muhimman wurare, domin inganta ilimi, kiwon lafiya da sauran muhimman sassa na tattalin arziki.

Ya kuma bayyana cewa Najeriya na da ƙwarewa da albarkatun da za su iya kera kayayyakin lantarki irin su mita, kebul, da transfoma a gida ba tare da dogaro da ƙasashen waje ba. A cewarsa, hakan zai taimaka wajen cimma dogaro da kai da kuma ci gaba mai ɗorewa a bangaren samar da wutar lantarki. Sabbin cibiyoyin horo da aka gina kuma za su bai wa matasa kayan aiki da ilimi na zamani domin ƙirƙira sabbin abubuwa da samar da ayyukan yi.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet