Addini
Tikitin Musilim-Musilim Ya Jawo Min Ƙiyayya a Coci – Remi Tinubu
Matar Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana cewa lokacin da mijinta ya tsaya takarar shugaban ƙasa a 2023 da tikitin Musulm–Musulm, ta shiga wani yanayi na ƙunci a cocinta na Redeemed Christian Church of God. A cewar ta, wannan mataki ya raba kan mambobin cocin, inda wasu suka nuna ƙiyayya gare ta, abin da ta bayyana a matsayin “yanayi mara dadi” Duk da haka, ta ce ta ci gaba da halartar ibada a wurin tare da dogaro da ƙarfafawar wasu dattawan coci.
Ta yi wannan bayani ne cikin sabon littafinta mai shafuka 52 da ta wallafa mai taken The Journey of Grace: Giving Thanks in All Things, wanda aka fitar don murnar cikar ta shekara 65. A cewar ta, duk da tsangwama daga wasu mambobin cocin, ta ci gaba da zama cikakkiyar memba har zuwa matsayinta na Mataimakiyar Fasto tun daga 2018. Ta ce ta ɗauki wannan jarabawar a matsayin darasi na ƙarfafa imani, inda ta bar Allah ya yi mata sakayya maimakon ta nemi ramuwar gayya.
Remi Tinubu ta kuma bayyana cewa tikitin Musulmi–Musulmi ya jawo suka daga kungiyoyin Kirista da dama a ƙasar, inda wasu ke ganin zai iya haddasa rarrabuwar kawuna. Amma magoya bayan mijinta sun dage cewa cancanta da daidaituwar siyasa ya kamata ya fi rinjayar tsarin tikitin. Duk da rikicin, Bola Tinubu ya ci nasara a zaben 2023 tare da mataimakinsa Kashim Shettima, inda suka kayar da Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Labour Party.
A ƙarshe, uwargidan shugaban ƙasa ta jaddada cewa ta riga ta yafe wa duk wanda ya nuna adawa da ita ko ya guje ta a lokacin zaben, tana mai cewa ta samu natsuwa da kwanciyar hankali ne ta hanyar yin godiya da kuma dogaro da maganar Littafi Mai Tsarki. Ta ce wannan darasi ya ƙarfafa ta wajen fahimtar cewa taimako ko goyon baya daga mutane na da iyaka, amma rahamar Allah ita ce abin dogaro na gaskiya.
