Featured
JAMB Ta Bankaɗo Yadda Aka Ɗauki Ɗalibai 2,658 a Jami’o’i Ba Bisa Ƙa’ida Ba
Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a ta Kasa (JAMB) ta gano yadda aka ɗauki dalibai 2,658 ba bisa tsarin hukumar ba a shekarar karatu ta 2024/2025. Hukumar ta bayyana cewa jami’o’i, kwalejoji da kuma polytechnic guda 17 ne suka aikata wannan laifi, inda mafi yawan su suka fito daga Abubakar Tafawa Balewa University Bauchi da ta samu 1,847 daga cikin haramtattun ɗaliban da aka ɗauka.
A jerin sunayen cibiyoyin da suka shiga cikin wannan matsala har da Osun State University (492), Abubakar Tafari Ali Polytechnic (148), Federal College of Animal and Health Production (66), University of Calabar (28), da College of Education, Oro (12), tare da wasu jami’o’in masu zaman kansu kamar Michael and Cecilia Ibru University da Redeemer’s University.
JAMB ta bayyana cewa duk wani ɗaukar ɗalibi da aka yi ba tarenda bin tsarin Central Admissions Processing System (CAPS)ba ana ɗaukarsa a matsayin haramtacce. Hukumar ta ce daliban da suka karɓi irin waɗannan guraben karatu ba za su cancanci yin hidimar ƙasa ta NYSC ba. Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya gargadi makarantu da jami’o’i da ke shiga wannan harkalla da cewa gwamnati za ta ɗauki matakin ladabtarwa, ciki har da kwace kadarori da hukunta jami’an da suka shirya lamarin.
An ƙaddamar da tsarin CAPS tun a shekarar 2017 domin tabbatar da gaskiya, adalci da cancanta wajen karɓar ɗalibai. JAMB ta jaddada cewa za ta ci gaba da sa ido tare da hukunta cibiyoyin da suka saba dokokinta, domin tabbatar da cewa tsarin karɓar ɗalibai a Najeriya yana gudana bisa gaskiya da nagarta.
