Featured
Ƴanbindiga Sun Kashe Mutum 1 Sun Sace 3 a Tsanyawa
Rahotanni daga ƙaramar hukumar Tsanyawa ta jihar Kano sun tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun kai hari a tsohon garin Yankamaye, inda suka kashe mutum guda tare da sace wasu uku. Lamarin ya faru ne da tsakar dare, lamarin da ya sake tayar da hankalin mazauna yankin.
Wannan bayani na zuwa ne daga ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Tsanyawa da Ghari, Injiniya Sani Bala Tsanyawa, wanda ya wallafa a shafinsa na Facebook, yana bayyana alhininsa kan wannan danyen aiki. Ya ce al’ummar yankin na fargaba ganin yadda hare-haren ke ƙaruwa a makonnin baya-bayan nan.
Kakaki24 ta tattara cewa matsalar tsaro ta fara ƙara ta’azzara a yankin Tsanyawa, inda ‘yan bindiga ke ketowa daga jihar Katsina mai makwabtaka. A makon da ya gabata ma, an sace mutum 18 a ƙauyuka uku na wannan gunduma, lamarin da ke kara tayar da hankali.
Gwamnatin jihar Kano da jami’an tsaro sun tabbatar da cewa suna ƙoƙarin ganin an daƙile waɗannan hare-hare. Hukumar tsaro ta ce an ƙara yawan jami’ai a yankunan da abin ya shafa domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.
