Featured
Saudiyya Ta Saki Ƴan Najeriya 3 Da Aka Tsare Ba Bisa Ƙa’ida Ba
Ma’aikatar Harkokin Waje ta sanar da sakin ’yan Najeriya uku da suka shafe watanni a tsare a Saudiyya bayan an tabbatar ba su da hannu a yunkurin safarar miyagun kayayyaki a Jeddah. Mutanen sun hada da Abdulhamid Sadieq, Maryam Hussein Abdullahi da Bahijah Aminu Abdullahi.
Rahoton ya bayyana cewa an danganta miyagun kwayoyin ne zuwa tikitin tafiyar mutanen ba tare da saninsu ba a Filin Jirgin Sama na Aminu Kano. Konsul din Najeriya a Jeddah, Amb. Muazam Nayaya, ya shiga lamarin cikin gaggawa, tare da sanar da Abuja da neman goyon bayan NDLEA domin bincike. Kakaki24 ta fahimci cewa an ba su lauyoyi, an kai musu ziyara a kurkuku, kuma an yi mu’amala ta kusa da hukumomin Saudiyya.
Bayan cikakken bincike, Saudiyya ta wanke su, inda aka sako su a ranar 14 da 15 ga Satumba 2025. An cire takunkumin tafiya daga bisani, inda Maryam da Bahijah suka dawo Najeriya a 5 ga Nuwamba 2025, yayin da takunkumin na Sadieq aka cire shi ranar 2 ga Disamba 2025, kuma ana kammala shirin dawo da shi gida.
Ma’aikatar ta gode wa hukumomin Saudiyya bisa hadin kai, tare da jaddada cewa lamarin ya nuna jajircewar Najeriya wajen kare ’yanta a ketare, kamar yadda ya kasance a cikin 4D Doctrine na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
