Featured
Kotun Ƙoli Tace Shugaban Ƙasa Yana Da Ikon Sanya Dokar Ta-baci a Kowacce Jiha
Kotun Koli ta Najeriya ta tabbatar da ikon shugaban kasa na bayyana dokar ta-baci a kowace jiha domin hana faduwar doka da oda ko hargitsi a kasa. Kotun ta ce shugaban kasa na da hurumin dakatar da Shugaba zababbe na wani lokaci yayin irin wannan yanayi na gaggawa.
Justice Mohammed Idris ya bayyana cewa sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulki na 1999 yana baiwa shugaban kasa damar daukar matakan gaggawa don dawo da zaman lafiya yayin da aka ayyana yanayi na gaggawa. Hukuncin ya biyo bayan karar da jihohi masu mulkin PDP suka shigar kan ayyana yanayi na gaggawa a Rivers, inda aka dakatar da zababben shugaba na jiha na watanni shida.
A cikin karar, masu shigar da kara sun tambayi kotu ko shugaban kasa na da hurumin dakatar da gwamnonin da mataimakan gwamnonin jihohi da kuma majalisun jihohi yayin ayyana yanayi na gaggawa. Kotun ta tabbatar da cewa masu kara basu nuna wani rikici mai karfi da ke bukatar kotun ta yi amfani da hurumin ta na asali ba.
Duk da haka, Justice Obande Ogbuinya ya nuna sabanin ra’ayi, inda ya ce shugaban kasa na iya ayyana yanayi na gaggawa, amma hakan ba zai ba shi hurumin dakatar da shugaba zababbe da aka zaba a jihohi ba.
