Connect with us

Featured

Tsohon Alkalin Alƙalan Najeriya Ya Rasu

Tsohon Babban Alkalin Ƙasa (CJN), Mai Shari’a Ibrahim Tanko Muhammad (mai ritaya), ya rasu yana da shekaru 71 a duniya. An tabbatar da rasuwarsa a ranar Talata, 16 ga Disamba, 2025, bayan fama da doguwar jinya a wani asibiti da ke kasar Saudiyya.

Mashawarcin Gwamnan Jihar Bauchi kan Yaɗa Labarai da Harkokin Sadarwa, Mukhtar Gidado, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya bayyana alhini matuƙa bisa rasuwar fitaccen ɗan jihar Bauchi da ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimar shari’a da gaskiya.

Gwamnan ya bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen alkalin da ya taka rawar gani a bangaren shari’a, inda ya yi aiki a Kotun Jiha, Kotun Ɗaukaka Ƙara, Kotun Koli, sannan daga bisani ya zama Babban Alkalin Ƙasar Najeriya daga shekarar 2019 zuwa 2022. Ya ce Tanko Muhammad ya shahara da kishin gaskiya, ladabi da biyayya ga doka.

A cewar gwamnan, marigayin ya samu lambar yabo ta ƙasa ta GCON sakamakon gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa tsarin shari’a a Najeriya. Gwamna Bala Mohammed ya miƙa ta’aziyya ga iyalan marigayin, ’yan shari’a da daukacin al’ummar Najeriya, tare da addu’ar Allah Ya jikansa da rahama, Ya sanya shi Aljannatul Firdaus.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet