Featured
Kasafin Kuɗi : Tsaro Zai Lashe Triliyan 5.41 Daga Cikin Kasafin Kudin 2026
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 Na Naira Triliyan 58.18 a gaban zaman haɗin gwiwar Majalisar Tarayya a ranar Juma’a, 19 ga Disamba, 2025 da misalin ƙarfe 2:30 na rana, inda ya ware Naira tiriliyan 5.41 domin ɓangaren tsaro—wanda ya zama mafi girman kaso a kasafin kuɗin ƙasar.
Tinubu ya bayyana cewa tsaro ne ginshiƙin bunƙasar tattalin arziki, jawo jarin masu zuba jari da kuma zaman lafiyar al’umma, yana mai jaddada cewa wannan ne karo na uku a jere da tsaro ke samun fifiko tun daga kasafin 2024 da 2025, sakamakon barazanar ta’addanci, fashi da makami, garkuwa da mutane da ayyukan ‘yan bindiga.
A cewar shugaban ƙasar, za a yi amfani da kuɗin wajen sabunta kayan sojoji, ƙarfafa ayyukan leƙen asiri, tsaron iyakoki da haɗin gwiwar hukumomin tsaro. Haka kuma, ya sanar da sabon tsarin yaƙi da ta’addanci da zai haɗa umarni guda, bayanan sirri da haɗin kai da al’umma.
Tinubu ya ƙara da cewa dukkan ƙungiyoyin makamai da ke aiki ba bisa doka ba—kamar ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane, kungiyoyin asiri da masu ɗaukar nauyinsu—za a ɗauke su a matsayin ’yan ta’adda, yana mai kira ga ‘yan majalisa da su goyi bayan kasafin domin dawo da amincewar jama’a da kare rayuka da dukiyoyi.
