Featured
Kwale-kwalen Ƴan Ci-rani Ya Kife a Tekun Gambia
Gwamnatin Gambia ta tabbatar da mutuwar aƙalla mutum 25 bayan wani kwale-kwale da ke ɗauke da ’yan ci-rani ya kife a gaɓar tekun ƙasar, yayin da ake shirin shiga sabuwar shekara. Jami’an tsaro sun ce kwale-kwalen na ɗauke da fiye da mutum 200, kuma har yanzu ba a gano da dama daga cikinsu ba.
Rahotanni sun bayyana cewa yawancin mutanen da ke cikin kwale-kwalen matasa ne daga ƙasashen Yammacin Afirka. Ana ganin sun shiga wannan tafiya mai hatsari ne domin ƙoƙarin ketare teku zuwa Turai, galibi ta hanyar tsibiran Canary na ƙasar Sifaniya.
Hukumomi sun ce irin waɗannan tafiye-tafiye na yawan faruwa ne da kwale-kwale marasa inganci da ke ɗauke da mutane fiye da ƙima, lamarin da ke haddasa mummunan haɗurra. Shugaban Gambia, Adama Barrow, ya bayyana cewa ƙasar na cikin jimami sakamakon wannan mummunan lamari.
