Connect with us

Featured

Dangaske ya yi alƙawarin tallafa wa ƙungiyar mata ƴan jarida domin ƙarfafa ayyukanta

An bayyana ƙungiyar mata ’yan jarida (NAWOJ) a matsayin masu ƙoƙarin bunƙasa ci gaban al’umma.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin fitaccen ɗan kasuwa a Jihar Kano, Alhaji Abubakar Sadiq Dangaske, a lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin ƙungiyar a ofishinsa.

Dangaske ya yaba da rawar da mata ’yan jarida ke takawa wajen wayar da kan al’umma, tare da jaddada cewa mata na da gagarumar gudummawa wajen gina al’umma mai inganci.

Ya kuma yi alƙawarin tallafa wa ƙungiyar domin ƙarfafa ayyukanta na ci gaban jama’a, musamman a bangaren jin ƙai da tallafa wa masu rauni.

A nata jawabin, Sakatariyar ƙungiyar ta ƙasa, Kwamared Wasila Ibrahim Ladan, ta ce sun kai ziyarar ne domin ƙarfafa dangantaka, neman shawarwari da tubarraki, tare da sanar da Dangaske ayyukan da ƙungiyar ke aiwatarwa a matakan ƙasa da jiha.

Ta kuma ce ƙungiyar na buƙatar haɗin gwiwar masu hannu da shuni domin ci gaba da ayyukan tallafawa mata masu ƙaramin ƙarfi, marayu da masu buƙata ta musamman.

Kwamared Wasila ta bayyana Dangaske a matsayin ɗan kasuwa mai kishin addini da al’umma, tare da yabawa irin gudummawar da yake bayarwa wajen tallafa wa ilimi da ɗaukar nauyin aikin Hajji da Umrah ga marasa galihu.

Ta kuma yi kira ga sauran masu hali a Jihar Kano da su yi koyi da irin wannan hali na taimakon jama’a, tare da yi masa addu’ar Allah Ya ƙara masa albarka da lafiya.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet