Featured
Matsalar Network Ne Yasa Muka Ƙi Amincewa da Dokar Tura Sakamakon Zaɓe Kai-tsaye – Akpabio
Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, Godswill Akpabio, ya yi ƙarin bayani kan gyaran dokar zaɓen ƙasar ta 2022 da majalisar ta amince da ita a makon da ya gabata. Gyaran dokar ya haifar da ce-ce-ku-ce a faɗin ƙasar.
Amincewar majalisar ta janyo suka daga ƴan adawa da ƙungiyoyi, waɗanda suka soki majalisar kan rashin amincewa da gyaran sashen da zai wajabta tura sakamakon zaɓe ta na’ura kai-tsaye. Masu suka na ganin hakan na iya buɗe ƙofa ga maguɗin zaɓe.
Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da wani littafi a Abuja a ranar Asabar, Akpabio ya ce ba a haramta tura sakamakon zaɓe ta na’ura ba. Ya bayyana cewa an cire kalmar “kai-tsaye” ne kawai, saboda matsalolin ‘network’ da ka iya hana tura sakamakon a wasu wurare.
