Featured
Ƴan Bindiga Sun Sace Dalibai 7 a Kwalejin Fasaha Ta Kaura Namoda
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun sace dalibai bakwai na Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Kaura Namoda a Jihar Zamfara bayan sun kai hari gidan da daliban ke zaune a wajen harabar makaranta. Shugaban Karamar Hukumar Kaura Namoda, Mannir Haidara Kaura, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da cewa an fara aikin ceto wadanda aka sace.
Wani dalibi mai suna Ibrahim Ahmad ya ce daya daga cikin daliban da aka sace ya samu ya tsere, lamarin da ya rage adadin wadanda ke hannun masu garkuwa zuwa shida, ciki har da maza uku da mata uku. Haka kuma wata kungiyar al’umma ta nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro a yankin tare da zargin wasu fitattun shugabannin ‘yan bindiga da haddasa hare-haren.
Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta tabbatar da sace daliban, inda ta ce jami’anta tare da dakarun Operation Fansan Yamma sun fara gudanar da aikin ceto. Kakaki24 ta ruwaito cewa rundunar ta ce harabar makarantar na cikin tsaro, yayin da ake ci gaba da kokarin kubutar da sauran daliban cikin koshin lafiya.
