Featured
Ana Zargin Ƙaramar Hukumar Gabasawa Da Dakatar Da Ma’aikaciyar Asibitin Zakirai Bayan Ta Yi Magana Da Manema Labarai
Ana zargin Karamar Hukumar Gabasawa da dakatar da Maimuna Alhasan, ma’aikaciyar sa kai a Asibitin Zakirai, tare da gurfanar da maigadin asibitin, Alhaji Me Mai, a caji ofis bayan sun yi magana a wani rahoton Freedom Radio.
Rahotanni sun ce sashen lafiya na karamar hukumar ne ya dakatar da Maimuna, wadda ta shafe shekaru tara tana aiki a asibitin ana biyanta Naira 3,000 kacal a kowane wata. Ana kuma zargin matakin ya biyo bayan bayanan da ta bayar kan halin da asibitin ke ciki.
Kungiyoyin matasa da na ci gaban garin Zakirai sun bukaci a yi wa Maimuna da Alhaji Me Mai adalci, tare da yin la’akari da gudunmawar da suke bayarwa wajen gudanar da ayyukan asibitin.
