Labarai
Cutar Sanƙarau Ta Hallaka Mutane Sama Da 20 A Jihar Kebbi
Aƙalla mutum 26 sun rasa ransu sanadiyyar ɓullar cutar sanƙarau a jihar Kebbi.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ambato kwamishinan lafiya na jihar, Musa Ismaila yana tabbatar da ɓullar cutar ranar Talatar nan.
“Muna fuskantar wani yanayi mawuyaci bisa ɓullar cutar da ke daɗa ƙaruwa,” kamar yadda Reuters ta ambato Ismaila yana cewa a wata sanarwar da ya fitar, inda ya bayyana cewa alamun cutar sun haɗa da zazzaɓi da ciwon kai da kuma sanƙarewar wuya.
An samu mutum 248 da ake tunanin suna dauke da cutar kuma an ɗauki jini da ruwan gwaji daga jikin marasa lafiya 11, sannan aka tura su babbar cibiyar bincike ta ƙasa a Abuja.
Biyu daga cikin ruwan da aka aika sun nuna cewa mutanen ba su da cutar, yayin da ake dakon sakamakon sauran samfurin ruwan, in ji shi.
Sakamakon hakan ne gwamnatin jihar ta raba magunguna a wuraren da lamarin ya shafa tare da samar da cibiyoyin killata waɗanda ke ɗauke da cutar da taimakon ƙungiyar agajin Doctors Without Borders a Gwandu da Jega da kuma Aliero, ƙananan hukumomin da lamarin ya shafa, in ji Ismaila.
Nijeriya na ɗaya daga cikin ƙasashen da ke fama da cutar a Afirka inda aka ba da rahoton cewa mutum 1,700 sun kamu da cutar a shekarar da ta gabata, kuma mutum 150 suka mutu cikin jihohi bakwai.
