Labarai
Zamfara: Majalisa ta dakatar da mambobinta bisa zargin su da hannu a ayyukan ta’addanci
Majalisar dokoki ta jihar Zamfara, ta sanar da dakatar da mambobinta 2 bisa zargin cewa suna da hannu cikin ta’addancin da jihar ke fama su.
Hakan na cikin wata sanarwar da daraktan yaɗa labarai na majalisar Mustapha Ja’afaru ya fitar da yammacin Talatar nan.
Sanarwar ta ce ƴan majalisar sun haɗar da Yusuf Muhammad Anka wanda ke wakiltar ƙaramar hukumar Anka da kuma Ibrahim Tukur Bakura mai wakiltar ƙaramar hukumar Bakura.
Sanarwar ta ce, dakatattun ƴan majalisar za su gurfana a gaban kwamitin majalisar na hukumomin tsaro da zai gudanar da bincike a kansu.
Haka kuma sanarwar ta ruwaito cewa dakatarwar ta tsawon watanni 3 ce gabanin majalisar ta kammala gudanar bincike akan zargin.
