Connect with us

Kasuwanci

Kano: Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da cibiyar sarrafa gwala-gwalai

A Alhamis ɗin nan ne ƙaramin ministan harkokin ma’adanai Dakta Uchechukwu Sampson Ogah, ya kai ziyayar aikin Kano domin duba wuri tare da ƙaddamar da aikin katafariyar cibiyar sarrafa wa tare da sayar da gwal.

Yayin ziyarar tasa Ministan ya kuma kai ziyara cibiyar Kasuwanci ma’adanai masanaantu da zuba jari ta jihar Kano KACCIMA.

Da yake jawabi ga manema labarai a cibiyar Dakta Uchechukwu Sampson Ogah, ya bada tabbacin cewa za su cigaba da yin aiki kafada da kafada da cibiyar domin ƙara haɓɓaka harkokin Kasuwanci.

Haka kuma ya ce, “Muna da alaƙa mai kyau da wannan cibiya, don haka na ziyarce su domin ƙara ƙarfafa ta kasancewar su manyan yan kasuwa”.

Da yake jawabi a madadin cibiyar ta KACCIMA, mataimakin shugabanta Ambasada Usman Darma, ya ce, “Tun da fari, sun nuna wa gwamnatin tarayya wurin da ya kamata a samar da cibiyar a cikin gari, amma sai gwamnatin ta sauya wurin wanda suke ganin hakan bai kamata ba la’akari da cewa ya kamata a ce wurin yana wurin da ke da tsaro”.

Ambasada Darma ya kuma ce, “Gwal kadara ce da za a iya sanya na miliyoyin Naira a aljihu ko jaka tafi duk inda ake buƙata ba tare da wani ya san menene a ciki ba, don haka ya kamata a samar da wurin sarrafa shi ya kasance mai tsaro da kyakkyawan yanayi”.

Haka kuma, cibiyar ta KACCIMA, ta bukaci gwamnati da ta yi laakari da bukatar tsaro a harkar gwala-gwalai ta fuskar karkato da aikin zuwa kasuwar baje-koli domin samun ingantacce tsaro tare da kyakkyawan yanayin aikin.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet