Featured
Shalƙwatar tsaro ta tabbatar da kashe jagoran ISWAP Al-barnawiy
Rundunar sojin Najeriya, ta tabbatar da mutuwar da rasuwar jigon ƴan tada ƙayar baya na ISWAP Abu Mus’ab Al-barnawiy.
Shugaban shalƙwatar tsaro Janar Lucky Irabo ne ya tabbatar da mutuwar tasa yau Alhamis yayin taron manema labarai da ya yi a birnin tarayya Abuja.
RFI Hausa ta wallafa a shafinta cewa Janar Irabor bai bayyana lokaci kuma yadda hallaka shi ba.
Haka ita ma ƙungiyar ISWAP ba ta ce komai ba.
Haka kuma ta ruwaito cewa, bayan mutuwar shugaban ƙungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ne Al-Barnawi ya ci gaba da jagoratar ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso gabashin Najeriya har ma da yankunan Tafkin Chadi.
