Labarai
Gwamnatin tarayya ta keɓe ranar hutun Maulidi
Gwamnatin Najeriya ta keɓe ranar Talata 19 ga watan Oktoban bana a matsayin ranar hutu domin tunawa da ranar da aka haihuwar Annabin SAW.
Hakan na cikin wata sanarwa Ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola ya fitar da yammacin jiya Juma’a.
Haka kuma ta cikin sanarwar ministan ya taya Musulmin Najeriya murnar zagayowar wannan wata mai ɗimbin daraja.
Ministan ya kuma buƙaci ƴan Najeriya da ke cikin gida har ma da waɗanda ke zaune a ƙasashen ƙetare da su cigaba da yiwa ƙasa addu’ar zaman lafiya da ɗorewar arziki.
