Labarai
Matsalar tsaro: Mata masu zanga-zanga sun rufe hanyar Gusau zuwa Kaduna
Wasu ayarin mata a ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara, sun rufe hanyar Gusau zuwa Kaduna a yau Alhamis.
A cewar masu wannan bore, hakan na a matsayin wani mataki na neman ɗauki mahukunta kan hare-haren da ƴan bindiga ke ci gaba da kaiwa a yankunan su duk da matakan tsaro da gwamnatin jihar ta ce ta dauka.
Matan waɗanda suke ɗauke da ƴaƴa har ma da kayayyakin su, sun yi zaman dirshan ne a kan titin tare da hana masu ababen hawa wucewa, lamarin da ya haifar da dakatar da zirga-zirga ga ɗaruruwan masu ababen hawa.
A zantawar guda cikin masu zanga-zangar mai suna Sadiya da jaridar PUNCH ta ce, sun yanke shawarar yin hakan ne kasancewar a koda yaushe ƴan bindiga na kai musu hari inda suke yi wa mata fyaɗe kuma babu wani mataki da jami’an tsaro suka dauka na kare su.
Haka kuma ta ce, “Mun tare hanya ne domin mu jawo hankalin gwamnati da jami’an tsaro su kawo mana dauki.”
Babbar hanyar ta Gusau zuwa Kaduna ta haɗa jihar zuwa wasu jihohi da dama na Arewa da na yankin Kudancin Najeriya.
