Connect with us

Labarai

Kano: Gwamnati ta kulle kamfanonin ƴan China 4

Gwamnatin Jihar Kano da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa reshen jihar Kano da kuma ƙungiyar masu sake sarrafa robobi da ledejin da aka yi amfani da su ACREWDON, sun kulle kamfanonin wasu ƴan kasar Sin guda 4 bisa zarginsu da yin aiki ba bisa ƙa’ida ba.

Jami’in kwamitin haɗin gwiwa kan tattara haraji na ma’aikatar kasuwanci ta jihar Kano Malam Adamu Umar ne ya jagoranci aiki da tsakar ranar Juma’ar nan.

Ya ce, an rufe wuraren ne sakamakon yin aiki ba tare da sahalewar mahukunta da ke da alaƙa da irin kamfanonin.

Malam Adamu Umar, ya kuma ce, kamfanonin ba su da wata takarda daga kowacce hukuma da ta basu izinin yin aiki, kasancewar tun a baya sun buƙaci su da su biya haraji kuma su je hukumasu, amma suka yi kunnen ƙashi.

A nasa ɓangaren, mataimakin shugaban kungiyar Kwadago ta ƙasa NLC reshen jihar Kano Kwamared Ado Salisu Riruwai, cewa ya yi “Ya kamata a ce ƴan asalin Jihar Kano ne suka mallaki wurin ba baƙin haure ba.”

Shi kuwa shugaban kungiyar masu sana’ar tara tsofaffin robobi da kwalaye Kwamared Salisu Ali Yarima yabawa gwamnati yayi kan ɗaukar matakin.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet