Ilimi
Ganduje ya baiwa mai lalurar gani takardar ɗaukar aiki
Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bai wa ma’aikatar ilimi ta jihar umarnin bai wa wani mai lalurar gani takardar ɗaukarsa aikin malanta.
Hakan na cikin wata sanarwa da sakataren ƴaɗa labaran gwamnan Abba Anwar ya fitar da yammacin yau Lahadi.
Sanarwar ta ce, wanda aka ɗauka aikin Dahuru Abdulhamid Idris, yana yin koyarwa ta sa kai a wata makaranta bayan da ya kammala karatu sa na koyarwa watau NCE.
Sanarwar ta kuma ruwaito gwamnan na cewa yayin ganawar gwamnan da Malam Dahuru, “A ƙoƙarina na inganta rayuwar al’ummar jihar Kano kuma a madadin gwamnatina, na amince a baka takardar ɗaukar aiki a ɓangaren koyarwa.”
Haka kuma sanarwar ta ce, gwamnan ya umarci Kwamishinan ilimi na jihar Muhammad Sanusi Sa’idu Ƙiru da ya tura malamin makarantar masu buƙata ta musamman da ke unguwar Tudun Maliki domin ci gaba da koyar da masu buƙata ta musamman.
