Tsaro
Neja: Ƴan bindiga sun hallaka mutane 18 a Maza-Kuka
Wasu gungun ƴan bindiga sun hallaka mutane 18 a kauyen Maza-Kuka da ke yankin ƙaramar hukumar Mashegu.
BBC ta ruwaito cewa ƴan bindigar sun far wa mazauna ƙauyen ne akan babura lokacin da suke yin sallar Asubah, inda suka buɗe wuta kan masallata.
Rahotanni sun bayyana cewa ƴan bindigar sun kuma jikkata mutane 20 tare da yin awon gaba da fiye da mutane 10.
