Labarai
Shugaba Buhari ya sauka a Saudi Arabia
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya sauka a birnin Riyadh na ƙasar Saudi Arabia domin halartar taro kan harkokin kasuwanci karo na 5.
Jaridar Internet ta Solacebase ta ruwaito cewa, shugaban na Najeriya ya sauka a filin jirgin saman sarki Khalid da ke birnin na Riyadh da misalin ƙarfe 11 na yamma agogon ƙasar.
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya samu tarbar tawagar gwamnatin ƙasar.
Haka kuma wasu cikin ministocin Najeriya ne suka yi masa rakiya domin halartar taron.
