Featured
Saɓa dokar aiki: Hukumar KAROTA ta kori wani jami’inta
Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA, ta kori wani jami’inta Jamilu Gambo, daga aiki bisa samun sa da saɓa dokar aiki.
Hakan na cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Nabilusi Abubakar Ƙofar Na’isa ya fitar a yau Alhamis.
Sanarwar ta ruwaito cewa shugaban hukumar Baffa Babba Ɗan-agundi ne ya bada umarnin korar tasa bisa samun sa da laifin fasa wa wani direban babbar mota Taya ranar Laraba a titin zuwa Hadejia.
Hukumar ta KAROTA ta bayyana laifin nasa a matsayin saɓa doka, inda bayan kammala wani zama hukumar ta yanke hukuncin sallamarsa daga aiki.
