Zamantakewa
Sayar da kududdufi: Masarautar Kano ta tuɓe wani mai unguwa
Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya sauke wani mai unguwa daga muƙaminsa.
Sarkin ya yanke hukuncin ne yau Alhamis bayan da aka gurfanar da wanda ake zargin a fadarsa.
Wanda aka sauke rawani nasa mai suna Malam Haruna Uba Sulaiman shi ne Mai Unguwar Ƙofar Ruwa B da ke yankin ƙaramar hukumar Dala.
Gidan rediyon Freedom, ya bada labarin cewa masarautar ta Kano ta samu tuɓaɓɓen mai unguwar ne da laifin yin Zamba ta hanyar sayar da wani kududdufi mallaki masarautar Kano ga wata mata.
Haka kuma ta ruwaito cewa, wakilin Arewa Malam Faruq Muhammad Yola ya shaida wa Sarkin cewa wannan ba shi ne karon farko ba da aikata irin wannan hali.
