Labarai
Shugaba Buhari ya sauka a ƙasar Scotland
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya sauka a birnin Glasgow na ƙasar Scotland.
A daren jiya Lahadi ne shugaban ya bar Najeriya domin halartar taron sauyin yanayi.
Hakan dai na zuwa ne bayan da shugaba Buhari ya yi kwanaki uku da dawowa Najeriya daga ƙasar Saudi Arabia halartar taron zuba jari da kuma gudanar da ibadar Umarah
A ƙasar ta Scotland Shugaba Buhari zai kasance guda cikin shugabannin fiye da ƙasashe 120 da za su halarci taron
Haka kuma ana sa ran cewa shugaban zai gana da shugaban ƙasar Amurka Joe Biden da shugaban ƙasar Faransa Emmanuel Macron.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ya ya fitar a Talatar makon jiya, ta ce, yayin taron shugaba Buhari zai gabatar da jawabi a wurin taron da tare da bayyana irin matakan da Najeriya ke ɗauka wajen rage ɗumamar yanayi.
