Tsaro
Jami’an tsaro sun kashe ɗan bindiga a wajen karɓar kuɗin fansa
Wasu jami’an tsaron hadin gwiwa a jihar Ekiti sun kashe wani mai garkuwa da mutane lokacin da ya je karɓar kuɗin fansa a bakin wani daji wanda ke tsakanin Ekiti jihar da Kwara.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Sunday Abutu, ne ya yi holin gawar mai garkuwa da mutanen a shalkwatar rundunar da ke birnin Ado Ekiti.
Ya ce, Jami’an tsaron sun yi kwanton ɓauna ne a bakin dajin lokacin da aka je biyan kudin fansar da suka kai naira miliyan biyu da dubu ɗari ɗaya don sako wani mutum.
Daga nan ne suka bi mutanen da suka je kaɓar kuɗin inda suka hallaka wanda ake zargin.
Wata majiya a jihar ta shaida wa manema labarai cewa, tawagar haɗin gwiwar sojoji da ƴan sanda da kuma ƴan bangar da Sarkin Fulanin Ekiti Alhaji Adamu Abashe ke lura da su ne suka yi nasarar hallaka shi.
