Connect with us

Labarai

Bashin albashi: Tsofaffin ma’aikatan Vision FM sun yi barazanar garzayawa kotu

Tsofaffin ma’aikatan rukunin tashoshin Vision FM da ke Kano su 13, sun buƙaci hukumar gudanarwar rukunin tashoshin da ta biya su bashin albashin da suke bin gidan rediyon fiye da naira miliyan 8 da dubu 500.

Cikin wata doguwar wasiƙa ta hannun Lauyan su B. A Muaz, ya buƙaci da a biya tsaffin ma’aikatan bashin da suke bi cikin kwanaki 7, wanda rashin cimma wannan matsaya, za su garzaya da maganar gaban kotu domin ɗaukar matakin sharia.

Tsofaffin ma’aikatan 13 sun ajiye aiki ne a watan Mayun da ya gabata.

Cikin takardar ajiye aikin da tsohon manajan tashar Malam Adamu Ladan ya jogaranta ga shugaban rukunin tashoshin Vision na birnin Abuja.

Tsofaffin ma’aikatan sun ce, an ɗauke su aiki ne bisa yarjejeniyar aikin wucin gadi na tsawon watanni 6 kafin ɗaga likkafar su zuwa cikakkun ma’aikata, tun a watan janairun shekarar 2019, wanda har wa’adin watanni shidan ya cika ba a kaiga yi musu komai ba.

Haka kuma sun ce duk da tunatarwar da suke wa hukumar gudanarwar gidan kan bashin da suke bi, amma ba wani tagomashi da aka yi kan wannan lamari.

Cikin wasikar da lauyan tsofaffin ma’aikatan ya aike wa manema labarai a daren Litinin ɗin makon nan, ya bayyana sunayen masu bin bashin da suka haɗar da tsohon manajan tashar Malam Adamu Ladan, Muhammad Garba, Ahmad Rufai Bello, Captain Abdullahi Adamu Bakoji, Saddik Muhammad Kiyawa, Aliyu Abubakar Getso, Mustapha Khamis, Malam Ashiru Shehu Kachako, Isyaku Turaki Maje, Lami Sumayya Murtala, Samira Adnan, da kuma Lami Shema.

Haka kuma sanarwar ta ce, an miƙa kwafin ƙorafi ga babban sifeton ƴan sanda na ƙasa da mataimakinsa na shiyya ta ɗaya da ke Kano da kwamishinan ƴan sandan Kano da daraktan hukumar tsaro ta DSS da kuma daraktan hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC shiyyar Kano.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet