Featured
Manyan dalilan da ya sa gwamnatin Buhari za ta cefanar da hukumar layin dogo ta Najeriya
Rahotanni sun bayyana cewa ƙaramar ministar harkokin sufuri ta Najeriya, Rukayyah Gbemisola Saraki, ta ce Gwamnatin tarayya za ta raba hukumar kula da layin dogo ta kasar tare da sayar da ita ga ‘yan kasuwa don inganta ayyukanta.
Rukayyah Saraki ta yi wannan jawabin ne a lokacin wani taron haɗin gwiwa na ƙasa da ƙasa da ya gudanar a birnin Paris ɗin ƙasar Faransa.
Ta ce matakin zai haifar da gogayya a ɓangaren sufurin jirgin ƙasa, tare da inganta kayayyakin more rayuwa da sauran kadarori.
Haka kuma ta yi kira ga ƴan kasuwa na ƙasashen waje a wurin taron da su lalubo hanyoyin zuba jari a fannin, tana mai cewa matakin zai sake farfaɗo da ƙimar kamfanin a cikin Najeriya da ƙasashen ƙetare.
“An sabunta alkawuran sufurin jiragen ƙasa a matsayin wani muhimmin ɓangare na sauyin zamantakewa da tattalin arziki.
“Abin lura shi ne tsarin tsare-tsare na shekaru 25 da aka yi niyya don gyara duk wani layin dogo da ake da su, da gina sabbin layukan dogo tare da haɗa sauran tashoshin jiragen ƙasa .
Sai dai sanarwa na zuwa ne a dai dai lokacin da ma’aikatan jiragen kasa su ka yi barazanar shiga yajin aikin gargadi na kwanaki 3 daga ranar Alhamis mai zuwa.
Ma’aikatan na neman a ƙara inganta tsarin albashinsu da jin dadinsu da kuma harkokin tsaro da suka shafi hanyoyin jiragen ƙasan.
