Connect with us

Labarai

Mun shirya yiwa Yahaya Bello ruwan ƙuri’u tamkar yadda mu ka yi wa Buhari – Al’ummar Kano

Wasu ƴan siyasa da malaman addini a jihar Kano sun sha alwashin yiwa gwamnan jihar Kogi Alhaji Yahaya Bello ruwan ƙuri’u a zaɓen shugaban ƙasa da ke tafe a shekarar 2023 tamkar yadda su ka yi wa shugaba Muhammadu Buhari.

Jagoran magoya bayan masu wannan yunƙurin Shuaibu Idris ne ya bayyana hakan, inda ya ce tun daga shekarar 2003 jihar Kano ke nuna goyon bayan ta ga shugaba Muhammadu Buhari amma a wannan karon za su koma goyon bayan gwamna Yahaya Bello da su ke burin shi ne zai gaji shugaba Buharin a zaɓen shekarar 2023.

Tun da farko masu wannan kudirin sun bayyana wannan furucin ne a ranar Lahadi a lokacin da su ka ziyarci gwamnan a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

Haka kuma sun bayyanawa gwamnan cewa masu goyon shugaba Buhari a shirye su ke da su baiwa dukkanin wani goyon baya da hadin kai domin ganin burinsa ya cika a siyasa.

A nasa ɓangaren gwamna Yahaya Bello godewa ƴan siyasar ya yi bisa yadda su ka yi la’akari da irin managartan ayyukan da ya ke yi a jihar Kogi wanda hakan ne ya sa su ka yi masa wannan kiran.

Hakazalika gwamna Yahaya Bello ya ce yana samun kiraye – kiraye daga ƙungiyoyi daban – daban akan ya amsa kira ya fito takarar shugabancin Najeriya a shekarar 2023. Ya ce tabbas ba zai watsawa wadanda su ke yi masa wannan kira ƙasa a ido ba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet