Labarai
Sokoto: Ƴan bindiga sun hallaka mutane 15 yayin wani hari
Rahotonni daga jihar Sokoto na nuni da cewa, kimanin mutane goma sha biyar ne suka rasa rayukansu sakamakon wani hari da yan bindiga suka kai wasu kauyuka biyu a jihar.
BBC ta ruwaito cewa, tuni gwamnan jihar Alhaji Aminu Tambuwal ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Litinin.
Gwamnan ya ce, an kai harin ne a yankunan ƙananan hukumomin Goronyo da Illela.
Haka kuma ya ce, ƴan bindigar sun hallaka mutanen ne a hare-haren waɗanda suka kai jiya Lahadi da kuma safiya yau Litinin.
Gwamnan jihar ta Sokoto, ya kuma miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga dangin mamatan tare da sauran mutanen da suka samu raunika.
